Hon Ibrahim Baba Hassan for House of Reps 2015.

Mafarauta Sun Kashe 'Yan Bindiga 75 A Jihar Adamawa A kokarin da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi na ganin sun kwace garin Maiha da ke jihar Adamawa ya ci tura, sakamakon kashe membobinsu sama da saba'in da biyar da 'yan banga suka yi a yankin. Idan ba a mance ba, a ranar Litinin din da ta gabata ne, 'yan kungiyar Boko Haram sun yi yunkurin kwace garin Maiha, inda har suka kashe jami'an sojoji da dama, ciki har da mai rike da mukamin Liyutanal, yayin da sauran suka gudu. Bincike ya nuna cewa bayan 'yan bindigan sun yi yunkurin kwace garin ne, sai farauta da 'yan bangan yankin suka hade kansu don inda suka yaki 'yan bindigan har ta kai ga sun yi nasarar kashe kimanin saba'in da biyar daga cikinsu. Sannan kuma sun bayyana cewa a shirye suke a duk lokacin da 'yan bindigan suka nemi sake dawowa domin kwatar garin.