ZAWIYYAR TIJJANIYYA FACEBOOK OF NIGERIA (POTISKUM BRANCH)

(1). Karka rinka yin fitsari a wurin da kake yin
wanka, domin hakan yana gadar da yawan
mantuwa. (2). Karka rika kwantawa barci bayan ka cika
cikinka da abinci, domin yin hakan yana gadar da
mutuwar zuciya. (3). karka rika yawaita kallan al'auranka ko ta
wasu, domin yin hakan yana sa dakikanci da
nauyin kwakwalwa wajen fahimtar abubuwa. (4.). kar karika yin bacci bayan sallar asuba har
sai rana tafito, domin yin hakan na janyo tsiya da
talauci. (5). kar ka sha madara bayan kaci kifi, domin yin
hakan yana gadar da kuturta. (6). karka ci ko sha alhali kana da janaba, domin
yin hakan makarohi ne, kuma yana jawo raunin jiki. (7) karka rika hassada ko munafunci da ha'inci,
domin suna da hatsari ga lafiya, sukan kuma haifar
da cutar hauka, gashi kuma suna bata ayyuka
masu kyau. (8). karka rika yawan kukan babu ko ka yi ta
tallan talaucinka afili. Yin hakan yakan dawwamar
da mutum cikinsa. (9) karka rika kwanciya barci alhali kana jin fitsari,
yin hakan yana haifar da mutuwar mazakuta. 10. kayi amfani dasu domin zasu amfane ka.
Allah yasa mu dace yabamu ikon aikatawa.