JIBWIS NIGERIA

ABOUT THE ORGANISATION

An organisation for the eradication of innovation and establishment of the Sunnah of the Holy Prophet (SAW). This group of Muslims and the organisation has been established as far back as 1977 in Nigeria, and its pioneering chairman was Alhaji Musa Maigandu Muhammad, and also its first grand patron was Late Sheikh Abubakar Mahmud Gumi and Late Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya served as its first National Chairman Ulama'u Council.

The organisation being the first of its kind in the history of Islamic propagation, scholarship, and championing the cause of Islamic religion courageously without fear, set aside tangible, concrete, and strong unambiguous aims and objectives, for the purpose of attaining its targeted goals.

The aims and objectives of the organisation are:

- Eradicating and eliminating ignorance from the society in general.

- Unity and brotherhood of the Muslim Ummah.

- Sensitizing and orienting Muslim Ummah on Islamic religion in relation to their developmental activities in their lives here and hereafter.

- Discarding, rejecting and throwing away of various unislamic beliefs in publications and in whatever form.

- Assuring, and affirming to the Muslim Ummah, that the holy prophet has accomplished and completed his mission fully, judiciously and diligently without leaving any matter unattended.

- Anybody claiming to be a prophet, or claiming that the prophet visits him, should be considered as a great original liar.

- Propagating Islam in Nigeria, right from the grass root (villages) level to international level.

- Acting vigorously and actively towards acknowledging the saying of the holy prophet (PBUH), specifically where he says: “whoever sees a negative thing, he has to change it with his hand, if he can't do that, then with his tongue, and if he can't do that, by his heart, and that is the weakest form of faith.”

- Maintaining that a proof must be from the book of Allah and Hadith of the holy prophet, and that proof should not be concealed under any circumstance.

The Organization, as an international Organization per se, has a lot of active organs that make the execution and running of its activities to go smoothly. Many sub committees are found in the Organization, and some of these committees include:

- First Aid Committee

- Da’awah Committee

- Seminar Committee

- Orphanage and less privileged committee

-Trustee Committee

- Education Committee e.t.c

EXECUTIVE COMMITEE

The current national chairman of the Organization is Sheikh Abdullahi Bala Lau, who was then deputy national chairman of the organization under the chairmanship of late Alh. Musa Maigandu Muhammad who succeeded him after his demise

- Deputy National Chairman: Alh. Ibrahim Na Alh. Azare

- National Chairman of Ulama Council: Sheik Sani Yahaya Jingir

- Deputy National Chairman of Ulama Council: Sheik Yusuf Sambo Rigachuku

- National Sectary General Of The Organization (JIBWIS): Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe

- Chairman First Aid Group: Alh Isa Waziri

- Deputy Chairman First Aid Group: Engr. Mustapha Imam Sifti

TRUSTEE COMMITTEE

- Sheik Yakubu Musa Hassan

- Sheik Alhassan Sa’idu Adam Jos

- Alh. Isa Waziri

JAMA’ATU IZALATIL BID'AH WAIQAMATIS SUNNAH, is an international Organization with adherents and followers all over the world, especially in Africa. In Nigeria, its original home, it has branches in the whole 36 state of the federation together with the FCT. Furthermore, the true teachings of Islam through the Organisation has crossed boarders from Nigeria to the neighboring Niger, Mali, Senegal, Togo, Cameroon, Chad, Burkina faso, Ginue, and many other African countries.

Its regular activities include:

- Active teaching of Islamic religion base on the true and authentic teaching of the holy prophet, may the peace and blessings of Allah be upon him, without resorting to following whims and caprices, prejudice and blind following.

- Massive teaching of true Islamic ideals.

- An annual/occasional Da'awah outings (national preaching) to villages and towns within and outside Nigeria, for the propagation of Islam.

- Periodic visits to prison for humanitarian and religious and to assist in securing the release of Muslim inmates convicted on minor offences through payment of fines and other possible assistance. - Periodic visits to hospitals and orphanages to assist indigent patients and inmates respectively. - Assist in the establishment of mosques and learning centers/schools. – maintaining various forms of publications, ranging from books, pamphlets, journals, magazines, newspapers, for enlightment, teaching and awareness among the Muslim Ummah.

- Maintaining a strong First Aid organ, for offering help to the Muslim Community.

The Organization has produced several scholars and students of knowledge all over the federation of Nigeria and beyond. It has the largest followers, especially those Muslims who truly act, only in accordance to the authentic teachings of the holy prophet.


HAUSA VERSION

Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (Jibwis)

Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da sunna

Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1977 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.

Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wag a gaci.

Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:

- Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.

- Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),

- Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.

- Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.

- Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).

- Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.

- Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.

- Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”

- Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).

Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hadar da:

Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hadar da:

- Kwamitin Da’awah.

- Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.

- Kwamitin Kula da Marayu

- Kwamitin Ilimi.

- Kwamitin Mutane Goma.

- Kwamitin Taimakon Gaggawa.

KWAMITIN ZARTASWA

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin gudanarwa tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.

- Alh. Ibrahim Na Alh. Azare: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.

- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya

- Sheik Sani Yaya Jingir: Shugaban Majalisar Malamai na kasa

- Sheik Yusuf Sambo Rigachuku: Mataimakin Majalisar Malamai na Kasa

- Alh. Isa Waziri: Shugaban Yan Agaji na Kasa

- Engr Mustapha Imam Sifti: Mataimakin Shugaban Rundunar Yan Aagaji na kasa

kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, da sauransu.

Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hadar da:

- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.

- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.

- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.

- Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.

- Kai ziyarori gidajen marayu da fursina da asibitoci, domin tallafar musulmai marasa galihu.

- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.

Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa da irinsu Mal. Hudu Chikaji. Koda ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu'a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira.
www.jibwisnigeria.org